Labarai
Gwamnatin Kano ta tuhumi shugaban asibitin Rimingado
Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ya umarnin a bada takardar tuhuma ga shugaban asibitin sha katafi da ke Rimingado
Malam Habibu Muhammad Auwal bisa nuna rashin kwarewa yayin gudanar da ayyukan sa.
Kwamishinan ya bada wannan umarnin ne a yau litinin lokacin da ya kai Ziyara yankin a wani bangare na zagaye duba aikin allurer rigakafi da yake yi fadin jihar nan.
Tsanyawa ya ce ya lura da rashin kula da aiki da shugaban asibitin ke yi, inda kuma a kasa amsa tanbayoyin da aka yi masa akan asibitn da yake kula
dashi.
Asibitin kashi na Dala ya fadakar da dalibai illar gobara
Asibitin AKTH zai gudanar da jarabawar kwarewa ga likitoci fiye da dubu
Mutumin da ya daure ‘ya’yan sa shekaru 3 a Kano ya rasu a Asibiti
Ya kuma nuna damuwar sa da cewar duk da irin kayan aikin da aka sanya a sibitin domin tallafawa al’umma amma basu gani a kasa ba ya yin ziyarar tasa.
Ya kuma ja hankalin sauran masu ruwa da tsaki a harkar lafiya da Su tabbatar Sun gudanar da ayyukan su kamar yadda ya kamata.