Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar gudanarwar asibitocin Kano ta gargadi asibitoci su daina ajiye kudi a hannun su

Published

on

Hukumar gudanarwar asibitoci ta jinahr Kano ta gargadi dukkanin asibitocin gwamnatin jihar da su daina ajiye kudi a asibitin, maimakon hakan ko yaushe su rika kaiwa banki ajiya, domin kaucewa abinda ka je ka zo.

Shugaban hukumar na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya yi wannan gargadin, yayin wani rangadi da ya kai cibiyar kiwon lafiya da ke Kunchi.

Ya bayyana cewa ajiyar kudin a hannun su, da kuma wasa-rere wajen alkinta kudaden zai kawo tarnaki wajen gudanar da harkokin asibitocin yadda ya kamata, kuma hakan ka iya kawo rashin gaskiya da adalci.

Dakta Ibrahim Tsanyawa ya kuma yabawa ma’aikatan cibiyar lafiyar da ke Kunchi, bisa yadda suke gudanar da ayyukan su yadda ya kamata, tare da cewa duk da irin kalubalen da suke fuskanta hakan bai sanya su gazawa ba.

Shugaban hukumar gudanarwar asibitocin jihar Kanon ya kuma bayar da umarnin sanya katifu a asibitin na Kunchi da kuma zanin gado, inda yayi alkawrin kara ma’aikata a asibitin, domin bunkasa harkokin kiwon lafiya.

Dakta Ibrahim tsanaywa ya kuma bayyana muhimmancin da duba kayayyakin aikin asibitoci ke da shi da kuma ziyarar ba zata, kasancewar hakan ne zai taimaka wajen ciyar da harkokin kiwon lafiya gaba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!