Labarai
Gwamnatin kano ta yi kira da babbar murya ga shugaban ƙasa da ya gaggauta ɗauke sarki daga gidan Nassarawa domin masalahar kano

Gwamnatin jihar kano ta buƙata shugaban ƙasar nan da ya ɗauke sarkin kano na sha biyar daga jihar kano domin samarwa da jihar masalaha, la’akari da yadda wasu ke anfani da wannan damar wajen neman tayar da husuma a faɗin jihar nan.
Mataimakin gwamnan jihar kano kwamrat Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya bayyana hakan, inda yace zaunar da sarkin kano na sha biyar a gidan sarkin na Nassarawa anyi shi da wata niya domin hana gwamnatin kano ta zauna lafiya da kuma ƙin yiwa al’ummar jihar abin da ya dace.
Haka zalika kwamrat Aminu Abdussalam Gwarzo yace zanga-zanga da al’umma suka fito a wannan satin, al’umma suna da hakkin fitowa domin nuna goyon bayan su kan abin da suke so, da suke buƙatar a cire sarkin kano na sha biyar daga gidan Nasarawa amma aka turo jami’an tsaro suka hana su tare da kama wasu daga ciki.
Gwarzo ya kuma ce suna kira ga shugaban ƙasa da ya gaggauta ɗauke sarkin kano na sha biyar daga cikin jihar Kano domin barin al’umma su zauna lafiya.
Gwamnatin kano ta ce yadda doka ta kawo tsohon sarkin haka doka ce ta kawo sabon sarkin dan haka abar doka tayi anfani.
You must be logged in to post a comment Login