Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Kano ya bawa matar shugaban Kasa sakon zu Tinubu kan halin matsin da ake ciki

Published

on

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi Kira ga gwamnatin tarayya da ta duba da irin halin da al’umma suke ciki na matsin rayuwa, don kawo karshen matsalar.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakuncin matar shugaban kasa Sanata  Remi Tinubu da tawagarta a fadar sa.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce ‘ya kamata matar shugaban kasar ta cigaba da taimakawa mata a bangaren ilimi kamar yanda tayi a jihar Lagos’.

Haka zalika mai martaba sarkin ya shawarci gwamnatin tarayya da tayi duba na tsanaki Kan batun dauke babban bankin kasa CBN da sauran manyan ma’aikatun gwamnatin tarayya zuwa jihar lagos.

Sarkin yace ‘kasancewar jihar kano garin ne  mai yawan  al’umma da kabilu daban-daban ya kamata  gwamnatin tarayya tayi duba wajen kawo cigaba a jihar kano’.

A nata jawabin mai dakin shugaban kasa Sanata Remi  Tinubu ta shedawa sarki cewa ‘tazo jihar kano ne domin halartar taro a jami’ar Maryan Abacha da kuma kardamar da wasu aiyuka a jihad kano’.

Freedom Radio ta rawaito cewa “a yayin ziyarar mai dakin shugaban kasa  Remi Tinubu ta samu rakiyar matar gwamnan jihar kano da mai dakin shugaban majalisar dattawa da kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin da dai sauran jami’an gwamnatin tarayya”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!