Labarai
Gwamnatin Kano tace zata ɗauki matakin kare aukuwar samun ambaliyar ruwa a faɗin jihar

Gwamnatin jihar Kano tace zata ɗauki matakin kare aukuwar samun ambaliyar ruwa a faɗin jihar, bayan da Hukumar kula da yanayi ta ƙasa tace za a samu iftala’in ambaliyar ruwan a wasu jihohi ciki har da nan Kano.
Kwamishinan muhalli Dakta Ɗahir Muhammad ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake ƙaddamar da aikin yashe magudanan ruwa a da ƙungiyar kasuwar Kantin kwari ta gudanar da safiyar yau Lahadi.
Shugaban riko na ƙungiyar kasuwar, Alhaji Abdullahi Sharu Na Malam yace sun ɗauki matakin ne don kare kasuwar daga iftala’in ambaliyar ruwan da ke aukuwa a kasuwar duk shekara.
Bikin ƙaddamar da aikin yashe magudanar ruwan dai ya samu halartar wakilcin ma’aikata tsara Birane ta jihar Kano, KNUPDA, da hukumar kashe gobara da jami’an tsaro na ƴan sanda da Bijilante da kuma Karota har da manyan ƴan kasuwar.
You must be logged in to post a comment Login