Labarai
Gwamnatin Kano za ta dauki matakan doka kan masu gini ko zuba Shara a magudanar ruwa

Gwamnatin Jihar Kano zata dauki matakan doka kan masu gini ko zuba Shara a magudanar ruwa dake jawo ambaliyar a birni da wajen Jihar.
Kwamishinan ma’aikatar Muhalli da sauyin yanayi na Jihar Kano Dahiru Muhammad Hashim ne ya bayana hakan da safiyar yau Jumma’a lokacin da yake kaddamar da Shirin yashe magudanan ruwa a shataletalen Baban Gwari dake nan Kano.
Dahiru Hashim, ya Kara da cewar kaddamar da yashe magudanan ruwa na cikin matakan kare ambaliyar ruwa da hukumar yanayi tayi hasashen samu a jihohin kasar nan ciki hadda Jihar Kano.
Ma’aikatar ta kuma bukaci sauran mazauna unguwanni su tabbatar da gyaran magudanan ruwansu kafin faruwar damuna Dan kaucewa ambaliya.
You must be logged in to post a comment Login