Labaran Kano
Gwamnatin Kano za ta fara amfani da na’urorin tsaro dan magance matsalolin da ake samu kan badakalar filaye
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta bijiro da tsarin sabunta mallakar filaye da gidaje don kare samun rigin gimu tsakanin al’umma.
Babban sakataren ma’aikatar kasa da tsare-tsare na Jihar Isyaku Umar ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da Freedom Radio.
Babban sakataren ya kuma ce za’a koma amfani da na’u’ra mai kwakwalwa ne, saboda tsaurara tsaro ga filaye da ma gidajen al’umma.
You must be logged in to post a comment Login