Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: Ganduje ya haramta sayar da gidaje da filaye barkatai

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta bada umarnin cewa daga ranar Lahadi, ba za’a ƙara sayarwa ko bayar da hayar gida ko fili ba a faɗin jihar, ba tare da sahalewar dagaci ko kuma wasu wakilai da aka aminta da su ba a hukumance.

Hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwa da kakakin sakataren gwamnatin Musa Tanko Muhammad ya fitar, wadda ta ce an dauki wannan mataki ne domin a inganta tsaro, tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jiharnan.

Ya kuma kara da cewa matakin na tafiya ne, ƙafa da ƙafa da abin da gwamnatin tarayya ta sanya a gaba na kawo karshen matsalar rashin tsaro da kuma ‘yan bindiga a wasu sassan kasar nan, kamar yadda BBC Hausa suka rawaito.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!