Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano za ta fara biyan diyya ga al’ummomin da aikin titi ya shafa

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da biyan diyya ga al’ummomin da aikin titin Kabuga zuwa Dayi ya shafa wanda gwamnatin tarayya ke gudanarwa.

 

Al’ummomin da abin ya shafa sun hada da mazauna Ungoggo, Rimin Gado, Tofa, Kabo, da Gwarzo.

 

Tun da farko a jawabinsa kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Ambssada Nasiru Sule Garo a lokacin da yake zantawa da al’ummar Ungoggo, Tofa, Rimin Gado, Kabo da Gwarzo, ya ce shirin ya nuna aniyar gwamnati na tabbatar da adalci da tallafa wa talakawa musamman wadanda ayyukan ci gaban al’umma ya shafa tare da raba su da muhallansu.

 

Garo ya ce, tun daga lokacin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince tare da fitar da sama da naira biliyan biyu domin biyan diyya ga mutanen kananan hukumomi biyar da abin ya shafa, aka bukaci duk wadanda suka cancanta da har yanzu ba a biya su kudadensu ba da su zo da takardun da suka dace ga ma’aikatar filaye da tsare-tsare don tantancewa da biyan diyya.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!