Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano za ta kaddamar da ayyukan gina manyan tituna 3

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta gudanar da ayyukan gina manyan tituna guda Uku a cikin kwaryar birni da kewaye.

 

Kwamishinan ayyuka da gidaje Injiniya Marwan Ahmad, ne ya bayyana hakan, ta bakin Daraktan tsare-tsare da bincike na ma’aikatar Injiniya Lawal Datti, ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da ‘yan kwangilar da ke neman gudanar da ayyukan a yau Litinin.

 

Titunan sun hadar da tsawaita su da buda titin Katsina daga shataletalan Baban Gwari zuwa Mill Tara, sai Titin Bela da kuma kara aikin titin Jaba zuwa Gayawa da ke yankin karamar hukumar Ungogo.

 

Haka kuma ya kara da cewa, za a gina hanyoyin da mutane masu tafiya a kasa za su rika bi a cikin birnin Kano.

 

Injiniya Sani Usman Suleiman na kamfanin gine-gine na Gerawa, wanda ya yi magana a madadin sauran ‘yan kwangilar, ya bada tabbacin cewa za su gudanar da ayyuka masu inganci tare da gamawa a kan lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!