Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano za ta kafa kwamitoci a ma’aikatu don magance cin hanci da rashawa
Gwamnatin Kano za ta kafa kwamitoci a ma’aikatu don magance cin hanci da rashawa
Babban Sakatare a bangaren Horaswa na ofishin shugaban ma’aikatan Jihar Kano Kabiru Shehu ya ce, gwamnati na yunkurin kafa kwamitoci a dukkannin ma’aikatun gwamnatin jihar Kano, domin magance yawaitar cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatun Gwamnatin.
Babban Sakataren ya bayyana hakan a yayin taron bita ga ma’aikatun Gwamnati domin kauce wa cin hanci da rashawa, wanda wasu kungiyoyi daga kasashen ketare suka shirya wanda aka gudanar ranar Talatar nan a jihar Kano.
Kabiru Shehu yace jihar Kano ita ce jiha ta farko a Najeriya da ta fara kirkirar hukumar yaki da cin hanci da rashawa, kuma jami’anta suka samu horo daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya yaba wa Gwamnati bisa daukar wannan mataki tare da kira gareta, da ta hada kai da Hukumar domin ta haka ne kwamitin zai samu nasara wajen gudanar da aikinsa.
A yayin taron an kuma gabatar da mukalu dangane da illar da cin hanci da rashawa ke haifarwa.