Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Rundunar yan sandan tayi bayani kan yadda Dino Melaye yayi yunkurin kubucewa

Published

on

Rundunar yan sandan kasar nan ta yi bayani dalla-dalla kan yadda Sanatan kogi ta Tsakiya Sanata Dino Melaye ya yi yunkurin kubucewa daga hannun su da yammacin jiya Talata.

 

A cewar rundunar yayin hakan ne domin kaucewa aikewa da shi garin Lokoja, inda kuma ta bada tabbacin cewar ko mai rintsi sai ta iza keyar sa zuwa garin Lokoja inda zai fuskanci hukunci kan zargin kisan kai.

 

Da yammacin jiya ne dai aka dauki senator Dino Melaye zuwa asibiti a birnin tarayya Abuja bayan da aka yi zargin cewar kafar sa ta karye bayan da yayi yunkurin dirgowa daga motar yan sanda.

 

An dai jiyo Dino Melaye na cewar shi fa ba za a kai shi garin Lokoja domin gurfanar da shi ba, inda ya ce ya na tabbacin ba za yi masa adalci ba ya kuma bukaci koma me zai faru ya faru a birnin tarayya Abuja amma ba a Lokoja ba.

 

Rahotanni na nuni da cewa Dino Melaye na da tsatsatsamar alakar siyasa da gwamnan Kogi Yahya Bello lamarin da ya sanya yaki amincewa da a damka shi a hannun gwamnan.

 

A daren Litinin din da ta gabata ne dai mai Magana da yawun rundunar yan sandan kasar nan Jimoh Mashood ya fitar da wata sanarwa inda ya ce  rundunar ta kuma damke Dino Melaye kuma za su aike dashi garin Lokoja domin fuskantar shari’a

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!