Labaran Kano
Gwamnatin Kano zata fara aiwatar da tsarin asusu bai daya a shekara ta 2020
Gwamnatin Kano ta ayyana watan Junairun shekara ta 2020 a matsayin lokacin da zata fara aiwatar da tsarin asusun bai daya na gwamnatin jihar Kano wato TSA
Babban sakataren ma’aikatar kudi zakari Sadiq Buda ne ya bayyana haka a jiya litinin yayin taron karawa juna sani ga daraktocin gudanarwa na hukumomin gwamnati da akantoci ma’aikatu daban daban.
Mal Buda wanda ya sami wakilcin kwamishin kudi , Shehu Na Allah Kura wanda ya ce wannan tsari na daga cikin hukuncin da suka yanke a wajen wata tattaunawa da hukumomin gudanarwa ma’aikatun gwamnati a taron da aka yi a watan Nuwamban shekara ta 2017.
Ya ce gwamnatin jiha ta bada kwangilar sanya wata manhajjar da zata taimakawa yiwuwar aikin ga ma’aikatun gwamnati jiha, domin su aiwatar da shi.
Da ya ke Magana wanda ya ke kula da shirin sanya manhajjar , Seth David Gana ya ce horon zai taimaka musu wajen amfani wannan manhajjar.
Mal Gana ya ce tsarin asusun guda na gwamnati zai taimaka inganta tsarin wajen tabbatar da gaskiya da adalci a yadda take kashe kudadenta.