Kasuwanci
Gwamnatin Kano zata kashe miliyan 200 don farfado da madatsar Ruwa ta Watari
Shirin bunkasa Noma da kiwo na jihar Kano (Kano state Agro Pastoral development project ), da Bankin Musulunci ke daukar nauyi ya ware kudi naira miliyan 200 don gyara madatsar Ruwa ta Watari dake karamar hukumar Bagwai don farfado da Noman Rani.
Shugaban shirin bunkasa Noma da kiwo na jiha Malam Ibrahim Garba Muhammad ne, ya bayyana hakan , inda ya ce hakan na daya daga cikin hanyoyin dakile matsalar da Annobar Corona zata haifar na karancin Abinci, da tsaftar sa a fadin jiha.
A wata sanarwa da Kakakin shirin Aminu Kabir Yassar , ya sakawa hannu aka rabawa manema labarai , shugaban shirin Malam Ibrahim Garba Muhammad, yace zuwa yanzu haka an fara shirye shirye gudanar da aikin wanda tuni ,Kwararrun Injiniyoyi da masana suka duba tare da tsara yadda aikin zai gudana, in da a bangare daya tuni an bada sanarwa ga dukkan masu ruwa da tsaki na noman rani da bunkasa shi da su nemi aikin.
Shugaban shirin ya kara dacewa “za a gyara hanyoyin ruwa da bututun da suka lalace tare da ma’adanar ruwa da take cike da cunkoson kasa wadda ke barazana ga Tafkin”.
Labarai masu Alaka.
Gwamnatin Kano zata Zamanantar da hanyoyin samar da Madarar Shanu
Shirin Bunkasa Noma da Kiwo na jiha zai fara yiwa dabbobi Allura ta Rigakafi
“Bugu da kari za a gyara Kadada sama da 150, da ta lalace don samar da wadataccen filin Noma”.
“An shirya fara gudanar da aikin a cikin watan Oktoban bana, wanda zai bunkasa kadada 1,000 da ake sa ran manoma 4,000 ne zasu amfana dashi wajen Noman Shinkafa da Alkama da kayan lambu,” inji Malam Ibrahim Garba Muhammad.
Shugaban ya ce duk da kokarin da gwamnatin jiha take wajen noman Shinkafa , noman na da bukatar fadada shi musamman wajen amfani da buntu na Shinkafa da manoma ke kona shi don amfani dashi a matsayin taki na noman rani.
Don haka shirin zai dauki matasa 1,000 tare da raba su kashi dari biyu rukuni -rukuni tare da basu tallafi da inji na aiki don samar da buntun Shinkafa mai hade da taki don siyarwa da manoma.Hakan zai bunkasa Noma da kiwo a jiha.Kana ya ce shirin karkashin hukumar ‘Sasakawa Global 2020’ zai bunkasa tare da habbaka noman Shinkafa da Masara, wanda za a zabi manoman su daga kananan hukumomi tare da basu horo da kayan aiki da wajen ajiye kayan da aka Noma da kuma yadda zasu yi kasuwancin su.
Ya ce tuni an gama cimma matsaya wanda da zarar an samu umarni daga Bankin Musulunci nan da dan lokaci mai zuwa ,shirin tare da hadin gwiwa da hukumar Sasakawa , za a fara wanda zai bunkasa samar da wadataccen kayan abinci a jiha.
You must be logged in to post a comment Login