Labarai
Gwamnatin Katsina ta amince wa kananan hukumomi kashe miliyoyin kudi wajen gyara maƙabartu
Gwamnatin jihar Katsina ta amince da kashe Naira miliyan Ashirin ga ko wacce karamar hukuma a jihar domin gyaran maƙabartun yankinta.
Gwamnan jihar Mallam Dikko Radda ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin Sarakunan gargajiya daga Masarautun Katsina da Daura.
A cewarsa a irin wannan lokaci na damuna da ake yawan samun lalacewar maƙabartu, akwai bukatar gwamnati tayi duba akan al’amarin, a wani bangare na ciyar da ilimin jihar gaba.

You must be logged in to post a comment Login