Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Lagos na aiki da mai rikon babban jojin kasa wajen inganta doka

Published

on

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ya ce gwmnatin sa na aiki tare da mai rikon babban jojin jihar don kasa kotu na mussaman da za’a dinga gurfanar da masu take dokokin toki.

Babajide Sanwo-Olu ya ce duk wanda aka kama da laifin za’a hukunta shi dai-dai da lafin da ya akiata.

Gwamnan na Lagos ya bayyana hakan ne a yayin addu’o’I na mussaman da kungiyar Kiristoci ta kasa CAN reshen jihar wanda aka yi a wata majami’a dake Gbagada a jiya Lahadi a Lagos.

Haka zalika Babajide Sanwo-Olu ya ce gwmnatin sa ba zata yi kasa a gwiwa ba, wajen hukunta duk wanda yake keta dokokin hanya, yana mai yin kira da masu abababn hawa da cewa ba wai kawai suna amfani da titinan jihar ba ne kadai, dole ne su dukkanin ka’idojin da aka gindaya don gudun haifar da cunkoso ababan hawa da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!