Labarai
Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun hutun Kirsimeti Dana Sabuwar Shekara
Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Laraba 25 da Kuma Alhamis 26 ga watan da muke ciki na Disamba a matsayin ranakun hutun bukukuwan Kirsimeti.
Haka zalika gwamnatin ta bayyana ranar Laraba 1 ga watan Janairun shekara Mai kamawa ta 2025 a matsayin ranar hutun Sabuwar shekara.
Hakan na cikin wata sanarwa da Ministan cikin gida Dr Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar ga manema labarai a yau.
Haka zalika ta cikin sanarwar gwamnatin tarayya ta taya al’ummar Kirista Murnar ranar ta Kirsimeti da Kuma Sabuwar shekara.
You must be logged in to post a comment Login