Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Hutun kirsimeti ne ya janyo karancin mai a Najeriya – IPMAN

Published

on

Ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa mai zaman kanta IPMAN reshen jihar Kano ta ce, ƙarancin man fetur da aka samu a kwanakin nan yana da alaƙa da hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara da aka yi.

Shugaban ƙungiyar Bashir Da malam ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio wanda yayi duba kan matsalolin man fetur, ƙarancinsa da kuma tashin farashin sa, baya ga batun janye tallafin sa da gwamnatin tarayya ke shirin yi a sabuwar shekara mai kamawa.

Alhaji Bashir Danmalam da ya kasance bakon shirin a yau ya ce, an samu karancin mai a kasar nan dalilin yadda ma’aikatan da ke yin dakon man daga depo depo zuwa sassan kasar nan sun ta fi hutu kamar yadda kowanne dan kasa ke morar hutun da gwamnati ta bayar don gudanar da bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.

Da yake ƙarin bayani kan batun janye tallafin manfetur da gwamnatin tarayya ke shirin yi a sabuwar shekara mai kamawa, Dan malam ya ce, “Tun bayan da gwamnati ta sayar da kamfanin mai fetur na kasa NNPC akwai dokokin da aka tsara da za su tafiyar da lamarin kuma akwai wasu hukumomi da suka haɗar da PPRA wanda kuma tuni an tsara yadda abin zai kasance”.

Ko da aka tambaye shi kan makomar kasuwancin su matuƙar gwamnatin ta aiwatar da kudurinta na janye tallafin man fetur din, shugaban ƙungiyar ta IPMAN ya ce, “Matsayar mu za ta ta’allaka ne kan yadda dokar sayar da man fetur a kasar nan ta kasance”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!