Labarai
Gwamnatin Najeriya ta bukaci jami’o’in kasar su hadi kai da bangaren masana’antun kasar
Gwamnatin tarayya ta bukaci jami’o’in Najeriya da su ci gaba da hadin kai da bangaren masana’antu a kasar nan domin habaka tattalin arziki da kuma harkar fasahar sadarwa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya yi wannan kira yayin bikin ya ye daliban Jami’ar gwamnatin tarayya da ke garin Dutsinma karo na biyu da day gudana jiya a harabar Jami’ar da ke jihar Katsina.
Muhammad Buhari wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar kula jami’o’in ta kasa Farfesa Abubakar Adamu Rashid ya ce shugaban kasar ya kalubalanci jami’o’in kasar nan da su fito da wata hanya da za su dinga hada hannu da masana’antu domin bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
Ya ce jami’o’in ne ya kamata su zama suna jan ragamar ci gaban al’umma, da fito da sabbin fasahar ciyar da al’umma gaba da kuma nuna shugabanci na gari domin amfanin al’umma baki daya.
Haka kuma ya yi kira ga daliban da aka ya ye da su yi amfani da ilimin da suka koya wajen bunkasa tattalin arzikin kasa ,inda kuma ya bukaci jami’ar da ta rubanya kokarin ta wajen gudanar da bincike wajen gano irin shuka da zai bunkasa harkar noma a kasar nan.