Labarai
Gwamnatin Najeriya ta karrama marigayi MK Abiola da Babagana a yau
Gwamnatin tarayya ta nanata kudurinta na ganin ta yi duk mai yiwuwa don ganin Dimokradiyyar kasar nan ta dore kan tafarkin da ya dace.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya sanar da hakan a safiyar yau a taron karramawa da gwamnatin tarayya ta shirya don girmama wasu manyan kasar nan da suka hadar da marigayi MKO Abiola da wanda ya yi ma sa takarar mataimakin shugaban kasa Babagana, da kuma fitaccen lauyan nan Gani Fawehimi.
Ya kara da cewa gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sha alwashin ci gaba da bin tsarin Dimokradiyya daidai da yadda ya dace, tare kuma da karrama wadanda suka cancanta.
Haka zalika ya shaida cewa kungiyoyi masu zaman kansu da na Kwadago da sauran ‘yan-siyasa da kuma ‘yan-jarida, su ne suka taimaka har wannan Dimokradiyya ta kai ga wannan lokaci.
Ya ci gaba da cewa nan gaba kadan akwai wadanda gwamnatin tarayya za ta karrama duba da irin rawar da suka taka don ganin kasar nan ta samu ci gaba mai dorewa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika lambar karramawar MKO Abiola ga dansa Kola Abiola, yayin da uwargidan marigayi Gani Fawehimi wato Ganiyat ta karba a madadin maigidan na ta, sai kuma Babagana Kingibe da ya karbi ta sa lambar girmamawar da kansa.