Labarai
Gwamnatin Nijeriya ta katse zirga-zirgar jiragen sama a Gabas ta Tsakiya

Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Nijeriya FAAN, ta sanar da jama’a cewa ana fuskantar tangarda a zirga-zirgar jirage zuwa da kuma dawowa daga kasashen Gabas ta Tsakiya sakamakon rufe sararin samaniya a wasu sassan yankin.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa wasu jirage da aka tsara su tashi daga filayen jiragen Nijeriya zuwa kasashen yankin, ciki har da na kamfanonin jiragen sama irin su Emirates da Qatar Airways, an soke su ko kuma an jinkirta tashinsu.
FAAN ta shawarci fasinjojin da abin ya shafa da su tuntubi kamfanonin jiragen samansu kai tsaye domin samun sahihin bayani kan halin da jiragensu ke ciki, yiwuwar sake tsara tafiya da sauran matakan da suka dace.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa tana sa ido kan lamarin tare da hadin gwiwa da hukumomin zirga-zirgar jiragen sama da kamfanonin jirage, kuma za ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon ci-gaba.
FAAN ta nuna rashin jin dadinta kan duk wata matsala da hakan ya jawo, tare da gode wa jama’a kan fahimta da hadin kai.
You must be logged in to post a comment Login