Ƙetare
Gwamnatin Sudan ta fitar da gargaɗin gaggawar samun ambaliyar ruwa

Gwamnatin Sudan, ta fitar da gargaɗin gaggawar samun ambaliyar ruwa a jihohi biyar bayan matakin ruwa a Kogin Nilu ya ƙaru kamar yadda rahoton gidan jaridar gwamnatin ƙasar Suna ya ruwaito.
Rahotonni sun danganta ƙaruwar matakin ruwa da babban Madatsar Ruwa na Ethiopia da aka buɗe a wannan watan.
Ma’aikatar nomar rani ta Sudan ta sanar da gargadin ne a baya-bayan nan inda ta ce, ya shafi jihohin Khartoum da River Nile da White Nile da Sennar da kuma Blue Nile.
Ma’aikatar ta yi gargaɗin cewa ruwa na iya mamaye gidaje da gonaki, tare da kira ga ɗaukar matakan gaggawa.
A kowacce shekara, matakin ruwa a Kogin Nilu ƴa na ƙaruwa a watan Agusta saboda ruwan sama mai yawa a tsaunukan Ethiopia.
You must be logged in to post a comment Login