Labarai
Gwamnatin Taraba ta haramta hawa Babura a Jalingo
Gwamnatin jihar Taraba, ta sanar da haramta amfani da babura kowane iri a Jalingo, babban birnin jihar.
Haka kuma, gwamatin ta sanya dokar takaita zirga-zirgar Babura masu kafa uku watau Adaidaita sahu daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 8:00 na dare.
Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar ya fitar, ta ce an ɗauki matakin ne sakamakon ƙaruwar ayyukan ta’addanci a kwaryar birnin Jalingo.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin kwamishina ƴan sandan jihar domin tabbatar da haramcin ya yi aiki kamar yadda ya kamata.
Gwamnatin ta ɗau alwashin kama wa da kuma hukunta waɗanda suka bijire wa haramcin hawa baburan, inda ta ce za a kwace babura da adai-daita sahun da suka saɓa dokar sannan a lalata su.
You must be logged in to post a comment Login