Kiwon Lafiya
Gwamnatin Taraba ta musanta zargin sayan makamai
Gwamnatin jihar Taraba ta musanta zargin cewa ta siyo makamai ta rabawa kungiyoyin sakai don farwa Fulani makiyaya a kokarin da take na kaddamar da dokar haramta kiyo a fadin jihar.
Gwamnan jihar Darius Ishaku ne ya bayyana hakan yau, a wani mataki na martani kan zargin da wani marubuci Dr. Aliyu Tilde yayi wa gwamnatin, inda yace gwamnatin jihar Taraba na shirye-shiryen zubar da jinin Fulani a jihar ta hanyar kirkiro da dokar haramta kiwo wacce zata fara aiki kwanan-nan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan Emmanuel Bello.
Sanarwar ta ce, babu kanshin gaskiya cikin zargin kuma babu wani lokaci da jihar ta sayo makamai domin rabawa ga matasa.