Labarai
Gwamnatin Taraba ta raba tallafi ga mutanen da rikicin manoma da makiyaya ya shafa

Gwamnatin jihar Taraba, ta raba tallafi ga mutanen yankunan da rikicin manoma da makiyaya ya shafa a Karamar Hukumar Karim Lamido, domin farfaɗo da rayuwar jama’a da rage musu radadin halin da suke ciki.
Wannan na cikin wata sanarwa da Gwamnatin ta fitar ta na mai cewa, kayayyakin da aka raba din sun haɗa da hatsi da taki da kananan injinan noman zamani don ƙarfafa aikin noma da bunƙasa amfanin gona a yankin.
Mutanen yankunan da suka amfana sun haɗa da Munga Lelau da Munga Dosso da Ngorore Jabu duk a Karamar Hukumar Karim Lamido.
Gwamnan jihar Agbu Kefas ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin samar da tsaro da yanayi mai kyau da zai bai wa jama’a damar komawa gidajensu su ci gaba da noma.
You must be logged in to post a comment Login