Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda aka sami arangama tsakanin manoma da makiyaya a Jigawa

Published

on

Akalla mutane 19 ne suka jikkata biyo bayan wata arangama tsakanin manoma da makiyaya a jihar Jigawa.

A yayin arangamar dai wani mutum mai suna Musa Mamman dan shekaru 55 ya mutu a kauyen Madamuwa dake karamar hukumar Guri dake jihar.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Abdul Jinjiri ya bayyana cewa tuni jami’an su suka cafke mutane biyu da ake zargi da hannu cikin tada rikicin.

Ya kara da cewa sauran mutanen da suka jikkatan tuni aka kai su cibiyar lafiya ta Gwamnatin tarayya dake Nguru don ceto rayukan su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!