Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya jihohi da kananan hukumomi sun raba sama da naira biliyan 700
Gwamnatin tarayya jihohi da kananan hukumomi sun raba sama da naira biliyan dari bakwai da arba’in da daya a matsayin kason su na rabon arzikin kasa a watan Ogusta
Babban sakataren ma’aikatar kudi Alhaji Mahmud Isah Dutse ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.
Ya ce kason watan Ogustan ya zarce na watan Yuli da naira biliyan ashirin da bakwai da miliyan hudu.
A cewar sa, an samu karin kudaden ne sakamakon karin adadin man da kasar nan ke fitarwa ketare, wanda ya tashi daga ganga miliyan 34 da dubu dari hudu a watan Yuli zuwa ganga miliyan 45 da dubu dari bakwai a watan Ogusta.
Da yake kasafta yadda aka tattara kudaden Alhaji Mahmud Isa Dutse ya ce; bangaren Albarkatun kasa ya samar da harajin sama da naira biliyan 451, yayin da sauran bangarorin da bana mai ba, suka samar da kusan naira biliyan 176.
Fasalin yadda aka yi rabon ya nuna cewa, gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 274 da miliyan 889 daga kudaden harajin mai ko kuma sama da kaso 54 , yayin da jihohi suka karbi sama da naira biliyan 139 su kuma kananan hukumomi suka karbi sama da naira biliyan 107 sai kuma jihohin da ke da arzikin man fetur da ke yankin Niger Delta wadanda suka karbi kaso goma sha uku wato sama da naira biliyan 53.
Haka kuma a cewar Mahmud Isa Dutse a bangaren harajin kayayyaki wato VAT gwamnatin tarayya ta karbi sama da naira biliyan 16 jihohi suka karbi kusan naira biliyan 55 sai kuma kananan hukumomi da suka karbi sama da naira biliyan 38.