Labarai
Gwamnatin tarayya na da kudurin tallafa wa marasa karfi- Minista Doro

Gwamnatin Tarayya, ta tabbatar wa da mutanen da ke cikin mawuyacin hali cewa, ta na da cikakken kudiri na taimaka musu da kuma tabbatar da tsaron rayukan su.
Ministan jin kai da rage talauci Bernard Doro, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Jos babban birnin jihar Plateau a ranar Litinin, Da ya ce manufar ma’aikatarsa ita ce tabbatar da cikar buri ga talakawa, masu gudun hijira, da sauran marasa galihu.
A cewarsa, ma’aikatar za ta inganta tsarin tallafi, fadada damar samun shirye-shiryen rage talauci, tare da tabbatar da cewa taimakon jin kai yana isa ga wadanda suka fi bukatar sa.
Ministan ya kara da cewa gwamnati za ta aiwatar da ayyukan jin kai ba a matsayin taimako ba, sai a matsayin hakkin da gwamnati ke da shi ga ‘yan Nijeriya, domin tabbatar da abinci, ilimi, da mafaka ga marasa karfi.
You must be logged in to post a comment Login