Connect with us

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutun ma’aikata

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu ga ma’aikata.

Hutun wani ɓangare ne na murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai.

Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.

A cikin wata sanarwa da Dr Shuaib Belgore, babban sakataren ma’aikatar ya fitar na bayyana cewa minista Rauf ya taya dukkanin ƴan Najeriya murnar bikin zagayowar shekarar tare da ba da tabbacin jajircewar gwamnati na magance duk wasu ƙalubale.

Rauf Aregbesola ya yi kira ga ƴan Najeriya da su hada hannu da gwamnati don tabbatar da samun ci gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!