Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutun bikin Sallah

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 6 da Litinin 9 ga watan Yunin bana a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan babbar Sallah.

 

Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya daukacin al’ummar Musulmi na gida da kuma na kasashen waje murnar zagayowar wannan rana.

 

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babbar sakatariyar ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, a ranar Litinin, ministan ya bukaci al’ummar musulmi da su ci gaba da yin koyi da sadaukarwa da imani kamar yadda Annabi Ibrahim A.S ya yi, tare da yin amfani da wannan lokaci wajen yi wa Nijeriya addu’ar zaman lafiya da karuwar arziki.

 

Ministan ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gyare-gyare da tsare-tsare da suka shafi al’umma da aka yi, domin ci gaban Najeiya a karkashin mulkin Shugaba Bola Tinubu, shi ne dawo da Nijeriya kan turbar ci gaba.

 

Yayin da yake yiwa al’ummar musulmi barka da zagayowar Sallah, Ministan ya bukaci dukkan ‘yan Najeriya da su hada kai da gwamnati mai ci a kokarinta na dawo da martabar Najeriya a matsayin babbar kasa guda daya mai dumbin al’umma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!