Labarai
Gwamnatin tarayya ta ayyana rasuwar Alhaji Sani Ɗangote a matsayin babban rashi ga ƙasa
Fadar shugaban ƙasa ta ayyana rashin marigayi Alhaji Sani Ɗangote a matsayin rashin da Najeriya ta yi ba wai iya Kano ba.
A cewar fadar marigayin nada kyakkyawar alaƙarsa da gwamnati.
Mataimakin shugaban ƙsa Farfesa Yemi Osibanjo ne ya bayyana hakan a yammacin ranar Laraba, yayin da ya ziyarci gidan Alhaji Aliko Dangote da ke Kano don yin ta’aziyya.
Farfesa Yemi Osibanjo ya kuma bayyana rasuwar Alhaji Sani Dangote a matsayin babban rashi baga iyalan sa kaɗai ba har ma da Najeria baki ɗaya
“Ya zama lallai a yi alhinin rashin sa duba da yadda ya sadaukar da kansa wajen ci gaban ƙasar nan da kuma al’umma”.
Da yake karɓar ta’aziyyar Alhaji Aliko Dangote ya godewa gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje musamman yadda yake kula da mahaifiyarsu.
You must be logged in to post a comment Login