Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Farfesa Shehu Alhaji Musa ya musanta zargin da ake masa na almundahana da kudin jami’a

Published

on

  • Farfesa Shehu Alhaji ya musanta zargin yin sama da fadi na miliyoyi
  • Farfesa ya zargi mambobin ASUU da kitsa masa manakisa.

Tsohon shugaban jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke garin Wudil a jihar Kano Farfesa Shehu Alhaji Musa, ya musanta zargin da wasu cikin malaman jami’ar ke yi masa na barnatar da kudaden makarantar ba bisa ka’ida ba.

Farfesa Shehu Alhaji Musa ya bayyana hakan a zantawarsa da wakilinmu Nura Bello da safiyar yau Litinin, inda tattaunawar tasu ta mayar da hankali kan kammala wa’adin zangon mulkinsa na kusan shekaru 10 a matsayin shugaban jami’ar.

Ya kuma ce, ‘wasu daga cikin shugabannin kungiyar malamai ta ASUU reshen jami’ar ne ke kokarin goga masa kashin kaji saboda wata rashin jituwa da ke tsakanin su’.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!