Kasuwanci
Gwamnatin tarayya ta bayyana alhini bisa fashewar tankar dakon Mai a Neja

Gwamnatin tarayya ta bayyana alhininta dangane da fashewar wata tankar man fetur a garin Essa da ke karamar hukumar Katcha a jihar Neja, da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.
Ta cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a jiya Laraba birnin tarayya Abuja, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici tare da mika ta’aziyya ga gwamnati ga iyalan wadanda abin ya shafa da kuma al’ummar jihar Neja.
Haka zalika Gwamnatin Tarayyar ta koka da cewa, duk da wayar da kan jama’a da kuma gargadin da ake ci gaba da yi, har yanzu mutane suna kasada da rayukansu, ta hanyar ɗibar mai yayin da tankunan dakon sa suka faɗi.
Mohammed Idris, ya ce tuni an umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, da ta hada karfi da Gwamnatin Jihar ta hanyar samar da kayan agaji da taimakon magunguna ga wadanda abin ya shafa da iyalan su.
You must be logged in to post a comment Login