Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mutane fiye da dubu sittin za su amfana da tallafin kayan abinci – NEMA

Published

on

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta bayyana cewa mutane dubu sittin da hudu da dari bakwai da sha biyar a jihar Neja ne za su amfana da tallafin kayan abinci daga gwamnatin tarayya.

Babban daraktan hukumar NEMA, Muhammadu A Muhammed ne ya bayyana haka yayin da yake mika kayan tallafin ga gwamnatin jihar ta Neja.

Muhammadu A Muhammed, wanda daraktan riko a sashen bada agaji da tsugunarwa na hukumar, Dakta Bandele Onimode ya wakilta ya ce, hukumar NEMA ta fitar da kayan abincin ne daga rumbun adana abinci na kasa da sahalewar shugaban kasa, Muhammadu Buhari don rabawa ga marasa karfi don saukaka musu radadin annobar corona.

Ya kara da cewa nau’o’in kayan abincin iri daban-dabam ton dubu biyar ne aka samar don rabawa mutane a jihar.

Shugaban hukumar ya nemi gwamnatin ta jihar Neja da ta wayar da kan jama’arta kan hanyoyin magance ambaliyar.

Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Mohammed Ketso wanda shi ya karbi kayan, ya yabawa gwamnatin tarayya tare da rokonta da ta tallafawa manoman rani a jihar don yaye musu kuncin da suka shiga sanadiyyar ambaliyar ruwan da ta shafesu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!