Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwa bisa matakin da ASUU ta ɗauka

Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwarta kan matakin da ƙungiyar malaman jami’o’i ASUU, ta ɗauka na tafiya yajin aiki, inda ta bayyana cewa bai kamata su tafi ba, alhalin ana tsaka da tattaunawa.
Gwamnatin, ta bakin Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa ta ce bai kamata ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, ASUU, ta fara raba goron gaiyatar tafiya yajin aiki ba tunda ana tattaunawa da duk kungiyoyin da abin ya shafa.
Ya ce gwamnatin taraiya na iya bakin kokarin ta na gyaran makarantun gaba da sakandire a fadin ƙasar nan.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa Alausa ya roƙi ƙungiyoyin da ke shirin tafiya yajin aikin da su dakatar da shirin su tunda gwamnati na tattaunawa da su.
You must be logged in to post a comment Login