Labarai
Gwamnatin Tarayya ta ce ba za a yi sulhu da ‘yan bindiga ba

Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya gargadi gwamnatocin jihohi da su dakatar da duk wata tattaunawa ko yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga, yana mai cewa hakan na raunana ƙoƙarin gwamnatin tarayya na yaƙi da ta’addanci.
A wata hira ta musamman da BBC Hausa, Janar Musa ya ce ‘yan bindiga ba sa mutunta yarjejeniyar zaman lafiya, kuma suna amfani da ita ne kawai don yaudarar gwamnati kafin su sake kai hare-hare. Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba ta biyan kuɗin fansa, yana karyata duk wani zargin da ke cewa ana biyan ‘yan bindiga domin sakin waɗanda aka sace.
Ministan ya ce ta’addanci a Najeriya ba na addini ba ne, domin Musulmi da Kirista duka na cikin waɗanda hare-haren ke shafa. Ya kuma bayyana cewa Najeriya na aiki tare da Chadi, Kamaru, Nijar da Mali, tare da amfani da fasahar zamani domin gano da murƙushe ‘yan ta’adda.
Ya bukaci jama’a su rinka kai rahoton duk wani abu da ake zargi, tare da guje wa duk wani taimako ga ‘yan bindiga, yana mai cewa kuɗin da aka samu ta hakan kuɗin jini ne. Janar Musa ya kammala da kira ga haɗin kan gwamnati, jami’an tsaro da al’umma domin dawo da zaman lafiya a ƙasar.
You must be logged in to post a comment Login