ilimi
Gwamnatin tarayya ta ce haryanzu darussan Lissafi da Turanci wajibi ne ga dalibai masu shirin shiga manyan makarantu

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa Turanci da Lissafi sun ci gaba da zama dole a O’Level
Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktar yada Labarai da hulda da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ta fitar a Abuja ranar Lahadi.
Ta ce an fitar da wannan bayani ne domin fayyace rashin fahimta da ya biyo bayan sabon tsarin da aka sanar na sauƙaƙe sharuddan karɓar ɗalibai a jami’o’i da sauran manyan makarantun gaba da sakandare.
You must be logged in to post a comment Login