Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya ta ce ta biya kimanin fiye da dala biliyan 5 ga jihohin kasar nan a rarar Paris club

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce ta biya kimanin dala biliyan 5 da miliyan dari hudu ga jihohin kasar nan a wani bangare na rarar Paris Club.

Minister kudi Zainab Ahmad ce ta tabbatar da baiwa gwamnonin kudin a yau Litinin a birnin tarayya Abuja.

Minstar ta ce adadin kudaden da aka baiwa jihohin idan aka juya su a kudaden Najeriya sun kai sama da tiriliyan daya da rabi, inda kuma ta ce an baiwa jihohin kudaden ne akan sharadi.

Wasu daga cikin sharudan sun hadar da, dole ne jihohi su biya albashi a karshen kowanne wata, kuma dole ne jihohi su biya kudaden da suka ara suka cike gibin kasafin kudi a shekarar 2016

Sauran sharuddan sun hadar da biyan Kason su ga hukumar ilimin bai daya ta kasa inda ita ma gwamnatin tarayya za ta bada nata kaso domin bunkasa bagaren ilimin firamare a kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,749 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!