Labarai
Gwamnatin tarayya ta dakatar da kafa sabbin jami’o’i da kwalejoji

Gwamnatin tarayya ta amince da dakatar da kafa sabbin jami’o’i, kwalejojin kimiyya da na ilimi na tarayya na tsawon shekaru bakwai
Ministan Ilimi kasar nan, Dakta Tunji Alausa, ne ya sanar da haka a jiya Alhamis bayan taron majalisar da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta.
Majalisar Zartarwa ta Najeriya FEC ta amince da dakatar da kafa sabbin jami’o’i, kwalejojin kimiyya wato polytechnics, da kwalejojin ilimi na tarayya na tsawon shekaru bakwai a fadin ƙasar.
A cewar ministan, matakin ya zama dole ne saboda damuwa da ake da ita kan rashin amfani da wasu cibiyoyin yadda ya kamata da karancin kayan aiki da kuma rashin ingancin ilimi a jami’o’in da ake da su yanzu.
You must be logged in to post a comment Login