Labarai
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da cibiyoyin tattara bayanai a jihar Zamfara
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da cibiyoyin tattara bayanai da zasu taimaka wajen samar da bayanai na yaki da ‘yan ta’adda a fadin jihar Zamfara.
Ministan sadarwa da bunkasa fasahar zamani na kasa Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, ne ya bayyana haka a lokacin da ya gana da gwamman jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle a birni tarayya Abuja, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun ministan Uwa Suleiman, ya bayyana.
Dr Isa Ali Pantami, ya ce cibiyoyin zasu fara aiki a watan Agusta mai kamawa domin tababatar da an samu bayanai da zasu rinka taimakawa hukumomi da jami’an tsaron kasar nan a kokarin da ake na yaki da ‘yan ta’adda.
A nasa jawabin gwamna Bello Matawalle, yace samar da sabon tsarin zai taimaka wajwen cike gidin da aka samu a baya na musamman ma na kyale kamfanonin sadarwa suna gudanar da aiyyukan su ba tare da tantance matsaloli da masu aikata laifi keyi.
You must be logged in to post a comment Login