Labarai
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da tsare-tsaren taffalin jin kai a yankin arewa maso gabas
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da tsare-tsaren taffalin jin kai a yanin Arewa maso gabashin Najeriya.
Shirin da aka kaddamar din dai zai fara ne daga shekarar bana zuwa 2021 zai kuma rika bada tallafi ga sassan da yan ta’adda suka tarwatsa.
Rahotanni sun bayyana cewa yake-yaken dake faruwa a yankin na Arewa maso gabashin kasar nan yana daya daga cikin 10 mafi muni da suka faru a duniya.
Rahoton ya kara da cewa sakamakon rikicin, mutane kimanin miliyan 7 da dubu dari 1 a yanzu haka suna bukatar rayuwa mai inganci, baya ga mutum miliyan biyar da rabi da suka samu tallafi a shekarar bara.
A yanzu haka dai sabon tsarin da aka samar zai kasance wata garkuwa da kuma gata ga masu neman taimako a yankin.
Da ya ke kaddamar da shirin, mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya yaba da irin gudunmowar da hukumar kula da yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya ta ke baiwa kasar nan da bagaren tallafawa rayuwar ‘yan gudun hijira.