Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya ta karbo basuka na fiye da naira Tiriliyan guda a shekaru 8

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce ta samu nasarar karbo basuka na fiye da Naira Tiriliyan guda cikin shekaru 8, ta hannun  hukumar dake kula da kadarorin gwamnati.

Ministar Kudi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad ce, ta bayyana hakan a yayin da take kaddamar da darkatocin hukumar ta AMCON a baban birnin Tarayya Abuja karkashin jagorancin Mr Muiz Banire mai darajar SAN.

Hajiya Zainab ta ce tun bayan kaddamar da hukumar ta AMCON a shekara ta 2010, hukumar ta sami nasarar karbo basuka na fiye da Tiriliyan guda daga masu cin bashi daga bankuna da halin yanzu suke fuskantar zargin cin hanci da rashawa.

Ministan ta kara da cewar, gwamnatin tarayya ce ta kafa hukumar ta hannun babban bankin kasa CBN, don ceto bankuna daga neman durkushewa, bayyan da wasu tsirarun mutane suka ci, amma suka kasa biya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,340 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!