Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kungiyar lauyoyi ta shirya gudanar da taron gaggawa kan dakatar da babban jojin kasar nan

Published

on

Kungiyar Lauyoyi ta kasa NBA ta shirya gudanar da taron gaggawa da majalisar zartarwar kungiyar kan dakatar da babban joji na kasa Walter Onnoghen.

Wannan bayanin na kunshe cikin sanarwar da babban sakataren kungiyar Jonathan Gunu Taidi ya fitar cewa majalisar zxartarwar kungiyar ne kawai za su halacci taron, don tattaunawa kan dakatar da babban jojin na kasa.

Kungiyar Lauyoyi ta kara da cewar, zata gudanar da taron ne a dakin taro na kungiyar dake babban birnin Tarayya Abuja da misalin karfe 12 na rana.

Daga cikin wadanda za su halacci taron akwai tsofafin shugabanin kungiyar da tsofafin manyan sakatarorin kungiyar ta NBA da kuma shugabanin kungiyar a matakan jihohin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!