Labarai
Gwamnatin tarayya ta kashe dala biliyan tara wajen gudanar da ayyukan raya kasa
Gwamnatin tarayya ta ce cikin shekaru uku da suka gabata ta kashe dala biliyan tara wajen gudanar da ayyukan raya kasa.
Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammed ne ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai, a wani bangare na shirye-shiryen fara taron hukumar kula da yawon bude ido na majalisar dinkin duniya shiyyar afurka karo na sittin da daya wanda za a fara yau a Abuja.
Ya ce gwamnati ta fi ba da fifiko wajen gyara tituna da shimfida layin dogo da gyaran filayen jiragen sama domin da cewa da zamani.
A cewar Alhaji Lai Muhammed, wasu daga cikin kudaden an kashe su ne ta hanyoyin bunkasa harkar bude ido wanda ya ce zai taimaka gaya wajen samar da kudade ga kasar nan.
Alhaji Lai Muhammed ya kara da cewa, ana saran wakilai dari da sittin da shida daga kasashe daban-daban da ministoci ashirin da shida da kuma wakilai dari uku da talatin da biyu daga kasar nan ne za su halarci taron.