Connect with us

Labarai

mutane 3 sun mutu a jihar Plateau sakamakon cutar amai da gudawa

Published

on

Gwamnatin jihar Plateau ta tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakon kamuwa da cutar amai da gudawa cikin mutum 90 da aka yi zargin suna dauke da cutar.

Kwamishinan lafiya na jihar Mistaa Kunden Deyin ne ya bayyana hakan a yau Litinin a babban birnin jihar Jos, inda ya kara da cewa cikin mutane 90 din da ake zargin suna dauke da cutar an tabbatar da kamuwar mutane guda uku.

Mistaa Kunden Deyin ya kuma kara da cewa mutanen sun rasa rayukan su ne sakamakon rashin isassun kayayyakin bada agajin gaggawa da za’a yi amfani da shi wajen tabbatar da cutar kafin tayi tsanani.

Ya kuma kara da cewa yajin aikin da kungiyar ma’aikatan Lafiya ta JOHESU ta tafi a kwanakin baya shi ma ya taka rawa matuka wajen mutuwar mutanen.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,834 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!