Labarai
Gwamnatin tarayya ta magantu kan ‘yan kasar da ke Iran bayan kaddamar da hare-hare

Gwamnatin Tarayya ta fitar da gargadi ga ‘yan Najeriya da ke zaune a Iran da ƙasashen Gulf bayan karuwar hare-haren soji a yankin.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya sanya hannu a ranar Asabar, gwamnatin ta ce tana bibiyar halin da ake ciki a kasashen Gabas ta Tsakiya, musamman hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a Iran da martanin da Iran ke yi a wasu ƙasashen Gulf.
An shawarci ‘yan Najeriya da su kasance masu faɗakarwa, su nisanci wuraren soja da na gwamnati, su rage zirga-zirga mara muhimmanci, kuma su guji taron jama’a da nuna rashin jituwa.
Haka kuma, an yi kira ga ‘yan Najeriya da su bi dukkan dokoki da umarnin hukumomin ƙasa domin kare rayukansu.
Jakadancin Najeriya a Tehran da ofisoshin a Qatar, Bahrain, Kuwait, UAE da Saudi Arabia suna a shirye don ba da taimako.
Gwamnati ta jaddada cewa lafiyar ‘yan Najeriya a ƙasashen waje ita ce babban abin da ake fifitawa, sannan ta yi kira ga bangarorin rikicin su koma teburin sulhu domin zaman lafiya a duniya.
You must be logged in to post a comment Login