Labarai
Gwamnatin tarayya ta magantu kan zargin El-rufa’i

Ofishin Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, ya karyata zargin tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, na cewa gwamnati na biyan kuɗin fansa ga ’yan bindiga.
Sanarwar ta ce, gwamnati ba ta taɓa biya ko bayar da wani abu ga ’yan ta’adda ba, sai ma gargadin da ta sha yi ga yan ƙasa da su guji yin hakan.
Gwamnatin ta bayyana cewa, rundunonin tsaro sun yi nasarar fatattakar yan bindiga a Kaduna, inda aka kashe tare da kama shugabanninsu da dama, abin da ya kawo aka samu zaman lafiya a yankin.
Ta ƙara da cewa waɗannan nasarori sun samu ne sakamakon sadaukarwar jami’an tsaro, don haka yin watsi da ƙoƙarinsu ba daidai ba ne.
Haka kuma gwamnatin ta roƙi yan siyasa da su guji mayar da batun tsaro siyasa.
You must be logged in to post a comment Login