Labarai
Gwamnatin tarayya ta nemi PENGASSAN da Matatar Dangote da su jingine rikicin da ke tsakaninsu

Gwamnatin tarayya, ta nemi ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da Iskar gas PENGASSAN da kuma matatar Dangote da su jingine rikicin da ke tsakaninsu, inda kuma ta kira su domin shiga tsakani.
A ranar Lahadi ne ƙungiyar ta PENSASSAN, ta sanar da fara yajin aiki a fadin Najeriya inda kuma ta yi niyyar farawa a yau Litinin sakamakon abinda ta kira korar ma’aikata da matatar Dangote ta yi bayan sun ayyana sha’awar shiga ƙungiyar.
Ministan Ƙwadago Maigari Dingyadi ya bayyana cewa wakilan ɓangarorin biyu za su gana da juna a shalkwatar ma’aikatarsa da ke Abuja.
Ministan, ya kuma nemi ɓangarorin biyu da su yi tunan muhimmancin ɓangaren fetur da Iskar gas ga Najeriya, saboda shi ne ƙashin bayan tattalin arzikin ƙasa.
Haka kuma sanarwar, ta kara da cewa, yajin aikin zai ajanyo babbar asara kuɗin shiga kawai zai jawo ga ƙasa ba, zai ƙaro wahalhalu ga ‘yan Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login