Connect with us

Labarai

Gwamnatin tarayya ta soke karbar haraji a kan hanya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta haramta karɓar haraji kuɗi hannu tare da hana tsayar da motoci a hanya domin tilasta biyan haraji, a wani ɓangare na sabbin ƙa’idojin aiwatar da dokokin haraji a ƙasar 

Shugaban Hukumar Haɗin Gwiwar Kuɗaɗen Shiga Olusegun Adesokan ne ya bayyana hakan ranar Talata a  birnin tarayya Abuja, yayin rattaba hannu kan ƙa’idoji da jagororin aiwatar da dokokin haraji.

Adesokan ya ce sabon tsarin an tsara shi ne domin kawo ƙarshen hanyoyin karɓar haraji marasa tsari, musamman a matakan jihohi da ƙananan hukumomi. 

Ya ce dokokin sun haramta duk wani nau’in karɓar haraji da kuɗi hannu tare da hana tsayar da motoci a hanya domin karɓar haraji.

Ya ƙara da cewa sabbin ƙa’idojin sun ware ƙananan sana’o’i da ke samun kuɗin shiga Naira miliyan 12 ko ƙasa da haka a shekara daga biyan haraji, yayin da sauran sana’o’in da ba sa cikin wannan tsarin za su biya harajin kaso ɗaya cikin ɗari na yawan kuɗin shigar su.

Ministan Kuɗi Wale Edun ya ce rattaba hannun kan ƙa’idojin na nuna fara aiwatar da gyaran tsarin haraji da majalisa ta amince da su a shekarun 2025 da 2026, yana mai cewa manufar gyaran ita ce faɗaɗa tushen haraji tare da kare ƙananan sana’o’i da tabbatar da gaskiya da daidaito a tsarin haraji.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!