Labaran Kano
Gwamnatin tarayya ta ware sama da naira biliyan biyu domin aikin dagwalon masana’antu a Kano
Gwamnatin tarayya ta ce, ta ware sama da naira biliyan biyu domin gudanar da magudanar dagwalon masana’antu da ke nan jihar Kano.
Babbar sakatariya a ma’aikatar muhalli ta kasa, Hajiya Habiba Lawal ce ta bayyana hakan a yau, a yayin ziyarar duba aiki data ke yi anan Kano a wasu manyan masana’antu uku dake jihar Kano.
Hajiya Habiba Lawal ta ce, sakamakon koke koken da al’umma ke yi ga masu ruwa da tsaki kan yadda warin dagwalon masana’antu ke Barazana ga lafiyarsu, hakan ya sanya gwamnatin tarayya ta amince da samar da magudanar ruwan don tace shi tare da sarrafa shi ta hanyoyin da suka kamata.
Ta Kuma ce, masana’antu ukun da ke jihar Kano sun hada da Sharada da Bampai da Kuma chalawa Wanda ake sa ran za’a kammala aikin a cikin shekara guda.
A nasa bangaren kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya bayyana kudirin gwamnatin jihar Kano na bawa Shirin goyon baya don kawowa al’ummar jihar Kano dauki.
Wakiliyar mu Madina Shehu Hausawa ta rawaito cewa a yayin zagayen duba aikin dagatai na yankunan da suke da masana’antu sin halarta tare da bayyana gamsuwar su.